“A Ƙarfafa Rundunar Haɗin-Gwiwa Ta Farar Hula Ta Najeriya Domin Tsaron Ƙasa” – Shugaban kasa, Farfesa Kailani Ya Buƙaci Gwamnati

Khailani1

Shugaban ƙungiyar farar-hula ta ƙasa (CJTFN), Farfesa Muhammed Kailani, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta baiwa mambobinsu kayan aiki domin magance matsalar tsaro a al’ummomin ƙasar.

Farfesa Kailani, wanda ya yi wannan kiran a jiya, ya yi kira ga Gwamnati da ta zo ta tallafa wa ƙungiyar farar-hula ta JTF domin kawar da ƴan fashi da makami a Najeriya.

Khailani2

A cewarsa, irin wannan mataki zai kawo zaman lafiya da haɗin kai, da kwanciyar hankali a ƙasar.

Ya ƙara da cewa, “A nan Kaduna, mun yanke shawarar kafa namu CJTF ne bisa ƙa’idojin aikin ƴansanda na Majalisar Dinkin Duniya; a cikin shekaru 16 da suka gabata, ana kashe ƴansanda da sojoji, ana kai wa talakawa hari da rana tsaka, don muka ga cewa muna buƙatar kafa wani civilian JTF, tare da haɗin-gwiwar hukumomin tsaro, kuma mun samu nasara sosai cikin shekaru 16 da suka gabata.

“Nasarorin kuwa, sun haɗa da daƙile tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da duk laifukan da suka dame mu a ƙasar nan, da kuma tabbatar da doka da oda, da kuma tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai ta hanyar tallafa wa jami’an tsaro, wanda muka yi a cikin shekaru 16, 17 da suka gabata.

“Na yi imanin cewa muna buƙatar mu tafa wa kanmu; a kan haka, muna kira ga shugabannin hukumomin tsaro, tun daga IGP zuwa CDS, zuwa babban daraktan DSS, da na Civil Defence, da sauran hukumomin soji da su cigaba da goyon bayan civilian JTF, domin mu isar wa ƙasar alkawari, ta yadda ƴan kasa za su kwana da idanunsu a rufe a Najeriya”.

Da yake jawabi ga mambobin CJTF, ya ci gaba da cewa, “Babu shakka jama’a kuna da hazaka; na yaba da dukkan ku; domin tarihi yana nan, idan kuka shiga daji ko kuma idan kun ba jami’an tsaro goyon bayan wajen kama ƴan fashi, da masu garkuwa da mutane, ku ne a sahun gaba.

“Ina ganin wannan wani abu ne mai ban al’ajabi da kuka ɗauka a tsawon shekaru. Muna kuma gode wa ƙananan hukumomin ƙasar nan 774, inda suke da DPOs, suna kuma baku goyon baya; yakamata su ci gaba da ba ku goyon baya.

“Don haka, wannan taro ne a matsayin wata taswirar dabaru don ƙara samar da zaman lafiya da haɗin kai ga Najeriya da ƴan Najeriya”.

Da aka tambaye shi kan ƙalubalen da mambobin CJTF ke fuskanta, sai ya amsa da cewa: “Akwai wasu lokuta da misali, wasu daga cikin mambobinmu na iya aiki da waɗannan jami’an ‘yan sanda, ko DSS; ba su gane wa, su (ƴan sanda) kawai za su kira ni daga ko’ina, cewa an kama mutanena, an saka su a cikin cell… Ina ganin ya kamata a daina”.

A cewarsa, “Idan akwai wani abu da jami’an tsaro ba su fahimta ba, to sa iya kiran shugabanninsu. Ya ci gaba da cewa: “Ku tambayi shugabanninku; kun ga yadda cikin jituwa, Kaduna, Abuja, duk Jihohi, suna aiki cikin jituwa a yanzu; saboda ina ganin sun gane cewa ba za su iya yin aikin su kaɗai ba.

“Idan ka lura da irin karfin da sojoji ke da shi a Najeriya a yau, yawan dukkansu kusan dubu 290 ne ko fiye; idan ka kwatanta da Masar suna da sojoji sama da miliyan 3. Mu muna da guda dubu 290 ne kawai; banda abin da ƴan sanda suke yi, da kuma hukumar DSS, don haka idan ka haɗa dukkan rundunonin da ke Nijeriya, ba na jin sun kai miliyan biyu. Kuma a nan ne muka shigo.

Ya kuma buƙaci jami’an CJTF da su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da da’a, inda ya buƙace su da su ƙarfafa haɗin-gwiwarsu da hukumomin tsaro da samar da zaman lafiya da haɗi-kai da kwanciyar hankali a Najeriya.

Related posts

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.