Taron Malaman Kur’ani: “Masu Adawa Da Dhirin Su Sake Tunani” – Farfesa Khailani Moh’d

IMG 20250126 WA0047

Wasu yan Nigeria na ta bayyana ra’ayoyin su game da taƙƙadama akan taron masana alkur’ani da ake shirin yi a Abuja, babban birnin tarayyar Nigeria.

IMG 20250126 WA0046

A yayin da wasu ke yabawa da shirin a wani yunkuri na haɗa kan al’ummar ƙasan, da kuma yiwa ƙasa addu’a wasu na sukar shirin, wanda a cewarsu ya na da nasaba da siyasa.

Farfesa Khailani Mohammed yana ɗaya daga cikin masu goyon bayan shirin, kuma a tsokacin da ya yi da ƴan jarida a ƙarshen makon nan ya ce: ” Na farko dai a ƙasar nan muna da haziƙai na karatun alkur’ani wanda ya fi na kasar Saudiyya, ko na ƙasar larabawa yawa. Amma duk da haka, babu wani taimako da Gwamnati ta taɓa yi musu.

“Na biyu, waɗanda suka kawo shawarar makarantun tsangaya ko na karatun allo a tsawon lokacin mulkin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda shine ya kawo shirin makarantun tsangayan, da kuma shirin tallafawa masu, sai aka samu akasin haka a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kuma aka soke wannan shiri na tsangaya. 

“To yanzu, a wannan mulki na President Bola Ahmed Tinubu, ake nema a farfaɗo da wannan shiri mai mahimmanci.

“Dama tuntuni muke ta magana akan cewa a maido da wannan shiri yadda za a yi makarantun allo da suke Nigeria da cewa akai musu makarantan Boko da na islamiyya, sa’an nan a rinƙa basu abinci yadda almajirai ba sai sun ringa yawo a tituna suna bara ba a cikin garuruwanmu, wanda ya jawo ana ta zagin mu ƴan Arewa. Wannan yana cikin abubuwan da za a tattauna a wajen taron, inda muke sa ran za a jawo hankalin Gwamnati zuwa wannan batun.

“Na uku, idan ka tafi ƙasar Saudiyya sau ɗaya ake kiran sallah sai kowa ya je masallaci; kuma kawunansu a haɗe yake. amm wani abun da doka tace.. amma mu a nan Najeriya ya kasance kowa yana yin abinda yaga dama a wannan addinin namu na musulunci. 

“Toh shiyasa su waɗannan wanda suka shirya wannan shiri, wato organizers, suka ce wannan lokaci ya yi wanda al’umman musulminmu, tunda  imanin mu ɗaya, addinin mu ɗaya, da mu zama al’umma ɗaya, kuma a haɗa kai yadda zai kawo zaman lafiya da cigaban addinin musulunci a Najeriya. 

‘Ina ganin wannan yana da kyau sosai, kuma a ganin waɗannan hafizan alkur’ani, duk za a haɗu a wajen taron za ,a gan su, kuma za a yi gasan da su kamar yadda aka saba. Kuma waɗanda suka ci gasan, abasu sakamako mai kyau, wanda ya dace.. kuma a san da zaman su, kuma menene ya kamata gwamnati tayi musu?

Toh mu a wajen mu, mun ga wannan abu ne mai kyau, cewa ana so ayi kira ne cewa Allah ya kare Najeriya daga abubuwan da suke faruwa; sa’an kuma a faɗakar da Gwamnati don su san da zamansu da kuma  halin da mutanen ƙasa ke ciki, na halin ƙunci ga mutane ke ciki; kuma in suna ji ne a da, amma ba su yi wani abu ba, toh yanzu suzo suyi to yanzu wannan dama ta samu ne wanda ya kamata ace kowane musulmi a maimakon mu koma bayan fage bane muna zarge-zarge ko ƙwarafe-ƙwarafe, muka ga cewa gara muje mu ga menene za a yi a wajen taron, ko na  alkairi ne wanda zai cima musulunci gaba”.

IMG 20250126 WA0045

Da aka tambaye shi kp me ya sa yake ganin al’ummar musulmi basa goyon bayan shirin, duk da cewa Sarkin Musulmi ya fito ya goyi bayan wannan tsarin, sai ya ce: “A ganina, rashin haɗin kan al’umman musulmai ne dalili. Baka ganin a ko maganar ganin wata na addinin musulunci, Mai alfarma, Sarkin Musulmi wanda shine Allah ya bashi ragamar shugabancin al’umman ƙasan nan, amma zaka ga akwai waɗanda suke ganin ai shi arkin musulmin ba shine ya cancanta ba kuma kuma duk sa’ilin da aka ga watan Sallah, zai fito yace an ga watan sallah, amma wasu suce a’a, ba zasu yi ba. Kuma Sarkin Musulmi zai fito yace a fito a yi, amma sai su ce sun ƙi… Saboda haka, muke ganin idan kowane musulmi yana ma wannan addinin namu ɗa’a, toh Allah yace shi kaɗai da manzonsa, annabi muhammadu (SAW); wannan shi ne musulunci.

“Saboda haka, ya kamata al’umman musulmai, mu zo mu haɗa kai, domin lokaci ne ya yi. Su waɗannan masu ƙwarafe-ƙwarafen, idan ka bincika, zaka ga su ne wanda basa son cigaban musulunci a Najeriya.. anamu fahimtar kenan.

“Saboda haka, muna kira a gare su, cewa idan dai ba wani abu bane, cewa indan ba su bane toh ba wasu, har da shi kansa Sheikh Bala Lau, wanda su suka fara wannan abu.. kuma nima da nake gaya maka wannan, nima zan saka kuɗi na a cikin shirin..

“Kazalika, muna fatan cewa wannan taron da za a yi, Sllah ya albarkace shi, ya kuma kawo mana cigaba a Najeriya; banda ma Nigeria, hadda ƙasashen larabawa ma zasu zo wannan taron, kuma da su za a yi..  saboda haka, banga dalilin da zai sa al’ummar musulmin ƙasar mu muzo muna ta  tada jijiyoyin wuya, ko kuma muna hura-hanci ba; abin da muke son dama tuntuni a zo a yi don asamu zaman lafiya da kuma ci gaba  

Don haka, duk waɗanda suke adawa da wannan shiri, da su ajiye wannan adawar, kuma mu zo mu gina wannan addinin musuluncin namu, don mu samu tsira gobe kiyama”.

Related posts

Leave a Reply