Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, zai ziyarci Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, a ranar 25 ga watan Yuni domin ƙaddamar da wasu manyan ayyukan more rayuwa guda biyu waɗanda ke nuna gagarumin ci gaba a tafiyar ci gaban jihar.

Daga cikin ayyukan, har da sabuwar gadar sama, da mashigar ƙasa da aka gina a kan titin Jos da Shendam, shiri na biyu da aka yi da nufin rage cunkoson ababen hawa, da haɓɓaka kasuwanci, da inganta zirga-zirgar birane.
Har ila yau, sauran ababen da aka tsara don ƙaddamar da shi, shi ne babban rukunin sakatariyar jiha, wanda aka gina don ƙarfafa harkokin mulki da nagartar gudanarwa a faɗin ma’aikatu, da sassan hukumomin jihar.
Gwamna Abdullahi Sule, tare da masu ruwa-da-tsaki, ana sa ran za su tarbi shugaban ƙasar, wanda ake ganin ziyarar tasa a matsayin wani gagarumin tabbaci na goyon-bayan Gwamnatin Tarayya na ci gaban ƙasa.
Tsohon Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Muhammed Abubakar Adamu, CFR, ya bayyana tsoma bakin shugaban ƙasar a matsayin “mai hangen nesa”, yana mai cewa ayyukan ba wai nasarorin ababen more rayuwa ba ne kawai, amma alamu ne masu ɗorewa na jagoranci mai ma’ana.
Ana sa ran bikin ƙaddamar da aikin zai samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da ƴan kasar, wanda suke kallon ayyukan a matsayin kawo sauyi ga jihar.
Sufeto-Janar Muhammed Abubakar Adamu (mai ritaya), a wani saƙo na bikin mai zuwa, ya yaba da jajircewar Shugaba Tinubu kan aƙidar dimokradiyya.
Ya buƙaci ƴan kasa da su cigaba da ruruwa a dimokradiyya, da ƙarfafa haɗin kan ƙasa, da kuma buɗe babbar fa’ida ta al’umma, ta hanyar gudanar da harkokin mulki ba tare da wata tangarɗa ba.
